fbpx
Saturday, June 19
Shadow

Kasar Ghana ta koro ‘yan Najeriya 541 gida inda tace sun cika mata kasa

Kasar Ghana ta Koro ‘yan Najeriya 541 gida da kuma ‘yan kasar Togo da Burkina Faso 2000 inda tace sun cika mata kasa ba gaira ba dalili.

 

An kama mutanen ne a Bolgatanga aka kaisu iyakar Aflao dake tsakanin kasashen Togo da Ghana.

 

Wani dake cikin mutanen yace suna kwance kawai sai aka kamasu aka kaisu bakin iyaka inda aka ajiye su a filin Allah har na tsawon mako daya.

 

Mutumin me suna Maxwell dan kimanin Shekaru 25 daya fito daga jihar Enugu ya kara da cewa da farko an ce sun yi yawa a kasar, daga baya kuma aka ce suna shaye-shaye da yiwa mata fyade.

 

Yace an bar ‘yan kasashen Togo da Burkina Faso sun tafi gida amma ‘yan Najeriya aka ce sai an zo daga ofishin jakadancin kasar dake Ghana, yace mutumin da aka kira yace baya nan sai nan da mako daya. Yace mako dayan yayi amma bai zo ba, dan hakane sai aka basu wasu fom suka cike, aka rabbatar basa cikin ‘yan gidan yarin da suka tsere daga gidan yatin jihar Imo.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *