fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Kasar Ingila da Lauyoyin ta sun kawowa Nnamdi Kanu dauki

Ofishin jakadancin kasar Ingila a Najeriya da wasu kwararrun lauyoyinta sun kawowa shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB,  Nnamdi Kanu dauki.

 

Sun nemi amincewar Nnamdi Kanu dan karbar ragamar kareshi a gaban kotu.

 

Lauyan Kanu, Aloy Ejimakor ne ya bayyana haka inda yace ya kaiwa Kanu takardun yarjejeniya inda ya nemi ya saka musu hannu. Yace hakan zai bude sabon babi akan shari’ar ta Kanu.

Lauyoyin kasar Ingilar na neman a saki Kanu saboda yanda aka kamashi ya sabawa dokar kasa da kasa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *