fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Kasar Ingila ta nemi yin magana da Najeriya kan Nnamdi Kanu amma Gwamnati taki bada hadin kai

Rahotanni sun bayyana cewa, wakiliyar kasar Ingila a Najeriya, Catriona Laing ta nemi yin magana da babban lauyan Gwamnati, Abubakar Malami kan kama Nnamdi Kanu amma ya ki bata hadin kai.

 

Lamarin ya farune a ranar Alhamis a wata haduwa da suka yi a wajan taro, Laing ta kawowa Malami maganar neman a Kanu, inda Malami yace mata ba zai aksa ta ba saboda ba abinda ya kaisu zaman kenan ba.

 

A baya dai kasar Ingila ta bayyana cewa, zata bi ba’a si kan ya da aka kama Nnamdi Kanu. Gwamnatin tarayya dai bata bada cikakken bayanin hanyar da aka bi wajan kama Nnamdi Kanu ba.

 

Ana zargin dai anwa Kanu wayau ne aka jawo hankalinsa wata kasar Africa da sunan za’a bashi wasu kudi, inda a nan aka yi ram dashi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *