fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Kasar Jamus ta bai wa DSS da wasu hukumomin tsaro motocin bas guda 10

A jiya ne hukumar manyan laifuka ta Jamus (BKA) ta ba da sabbin motocin bas kirar Toyota Hiace guda 10 ga hukumomin tsaro na tarayyar Najeriya.

BKA wata hukuma ce ta tabbatar da doka ta Tarayyar Jamus da ke da alhakin yakar tawaye a duniya, fataucin miyagun kwayoyi, fataucin bil adama, laifuka ta yanar gizo, gami da garkuwa da mutane da fashin teku.

An gudanar da shirin ne a Germaine Auto Center, Lekki, Lagos, inda karamin jakadan Tarayyar Jamus a Legas, Dr. Bernd von Muenchow-Pohl, ya mika motocin 10 ga hukumomin tsaro.

Hukumomin tilastawa wadanda suka amfana sun hada da DSS, Hukumar Hana Fataucin Mutane ta Kasa, Hukumar EFCC, Hukumar Yaƙi da Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa da Rundunar ‘Yan sandan Najeriya.

Daraktan DSS a Legas, Mista Egbunu J. Yusuf; Mataimakin Kwamandan Shiyyar EFCc, Emeka OOkonj; Shugaban Shiyyar Legas, NAPTIP, Ganiyu Aganran; DCGN, NDLEA, Adeyemi Adeofe; da DCP na NPF Tunji Disu, sun kasance a gurin kuma sun karɓi bas ɗin a madadin hukumomin su.

An ce BKA tana da haɗin gwiwa na dindindin tare da hukumomin tilasta bin doka da oda na Najeriya, wanda bai takaita da matakan aiki kawai ba, amma kuma ya shafi horaswa, tallafin fasaha da samar da kayan aiki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *