fbpx
Friday, April 23
Shadow

Kasar Japan Ta Tallafawa Bangaren Kiwon Lafiya Na Najeriya Da Biliyan N41

Gwamnatin Tarayya ta ce Gwamnatin Japan ta ba da dala miliyan $18.2 (kimanin biliyan N40.6) don tallafawa bangaren kiwon lafiya na Najeriya.
Karamin Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare na Kasa, Clem Agba ne ya bayyana hakan jiya a Benin yayin ziyarar da ya kai asibitin koyarwa na jami’ar Benin.
Ya ce ya kawo ziyarar ne domin tantance amfani da biliyan N49 da Gwamnatin Tarayya ta saki ga cibiyoyin kiwon lafiya na tarayya 52 a kasar.
Ya ce tallafin na Japan zai zo ne ta hanyar kayan aiki da kuma kara karfin ma’aikatan kiwon lafiya.
Ya ce an samu wannan tallafi ne daga ziyarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya kai wa Firayim Ministan Japan a shekarar 2019.
“Muna kuma aiki tare da USAID kuma na sanya hannu kan waccan yarjeniyoyin inda su ma suka ba mu na’urar iska 200 kuma ina sane da cewa asibitin kwararru na Irrua ya samu uku sannan UBTH ma sun samu uku daga cikin su 200 da muka yada a sake a fadin kasar,” in ji shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *