fbpx
Thursday, May 6
Shadow

Kasar Saudiyya ta baiwa mata damar shiga aikin Soja

Jaridar Saudi Gazette ta ƙasar ta ce za a fara karɓar takardun mata masu son shiga aikin soja daga 13 ga Fabrairu zuwa 18 ga Fabrairun wannan shekarar kamar yadda hukumar da ke kula da harkokin soja ƙarƙashi ma’aikatar harkokin cikin gida ta sanar.

Kwalejin Tsaro na King Fahd makaranta ce ta koyon aikin soja a Riyadh.

Ɗaliban da suka kammala karatu a wannan makaranta na iya samun aiki a bangarorin tsaro da dama na ƙasar kamar ma’aikatar harkokin cikin gida da hukumomin da ke sa ido kan safarar ƙwayoyi da rundunar tsaro ta civil defense da hukumar shige da fice da ta gidan yari da dai sauran su.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *