fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Kasar Sweden ta gargadi Gwamnatin Buhari, Amnesty international ta yi Allah wadai da dakatar da Twitter a Najeriya

Kasar Sweden ta yi martani kan dakatarwar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari yawa Twitter a Najeriya.

 

Tace ya kamata a girmama ra’ayin Jama’a. Kasar tace ‘yan Najeriya nda damar bayyana ra’ayoyinsu da kuma damar samun Labarai.

 

The tweet reads, ”Nigerians have a constitutional right to exercise their freedom of expression and a right to access of information.

”This must be respected. Safeguarding free, independent media and civic spaces for democratic voices is an important part of Sweden’s #DriveForDemocracy #TwitterBan

 

A bangaren Amnesty international kuwa ta yi Allah wadai da lamarin ne.

 

Ƙungiyar Amnesty International mai fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam ta yi tir da dakatar da shafin Twitter a Najeriya, inda ta ce shafin na bai wa ƴan Najeriya da dama ƴancin tofa albarkacin bakinsu da samun bayanai.

Ƙungiyar ta yi kira ga hukumomin Najeriya da su gaggauta soke dakatarwar da ta ce ta saɓa wa ƙa’ida kuma za ta hana ƴan jarida ƴancinsu.

Amnesty ta ce matakin bai dace da haƙƙin Najeriya na bai wa al’ummarta dama da ƴanci ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *