fbpx
Saturday, April 17
Shadow

Kayayyaki da kadarori na miliyoyin Naira sun lalace yayin da shaguna suka kama da wuta a Osogbo

Shaguna da sauran kadarori na miliyoyin nairori a ranar Lahadi sun kone a kasuwar Orisunmbare, kusa da bankin Wema a Osogbo.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta kasa reshen jihar Osun, Adijat Basiri ne ya bayar da labarin barkewar gobarar ga yan jaridar, inda ya sanar da cewa gobarar ta fara ne daga karfe 4 zuwa 4:30 na yamma.
Basiri ya ce lokacin da gobarar ta tashi, ba a gano ta a kan lokaci ba har sai da ta yadu sosai ta yadda ba za a iya shawo kanta ba.
A cewar shi, “Mutanen yankin sun yi matukar kokarin kashe wutar amma lokacin da ta yadu ta yadda ba za a iya shawo kanta ba, an kirawo rundunar don ceto lamarin.
A wani Labari makamancin wanan, hutudole.com ya ruwaito muku yanda aka samu Gobara a kasuwar jihar Yobe.
“Lokacin da jami’anmu suka isa wurin, da hanzari suka fara aiki kuma cikin‘ yan mintuna, aka kashe wutar amma bayan ta yi mummunar barna ga kayayyakin da aka ajiye a cikin shagunan.
“Ya dauki ƙoƙari sosai daga ɓangarenmu don kashe wutar amma halin da ake ciki yanzu ana kan bincike.”
Ya bayyana cewa ana amfani da shagunan ne domin adana akwatuna, kananan fayafai, man ja da sauran abubuwa wadanda duk sun ci wuta.
“Tunda duk abubuwan da ke cikin ajiyar na iya ƙonewa, bai ɗauki lokaci mai yawa ba kafin ya yi saurin haifar da babbar wuta.”
Har zuwa lokacin wannan rahoton, ba a iya gano musabbabin tashin gobarar ba amma PRO ya bayyana cewa za a gudanar da bincike don gano musabbabin tashin gobarar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *