fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Kimamin maza 89 ne suka sha duka da tsangwama daga matansu cikin watanni a Jihar Legas – Kwamishinan Harkokin Mata

Gwamnatin Jihar Legas ta ce maza 89 ne suka ba da rahoton cewa matansu suna musguna musu a cikin gida tsakanin shekarar 2020 da zangon farko na 2021.

Kwamishinar harkokin mata da rage talauci (WAPA), Cecilia Bolaji Dada, ce ta bayyana hakan a ranar Talata a taron manema labarai na ministocin don bikin cika shekara biyu da Gwamna Babajide Sanwo-Olu yayi a ofis, wanda aka gudanar a Ikeja, Legas.

Kwamishinan ta ce, a shekarar 2020, maza 46 ne suka kawo rahoto a ma’aikatar cewa matansu na keta musu haddi.

Ta kara da cewa a zangon farko na shekarar 2021, maza 43 ne suka kawo rahoton matansu, wannan shine dalilina da ya sa yawan mazan yakai 89 a kasa da shekaru biyu.

Dada, ta bayyana cewa mata 664 ne mazajensu suka ci zarafinsu a Legas a shekarar da ta gabata, kamar yadda shari’ar ta ruwaito a WAPA.

Ta kara da cewa, wato mata 378 ne mazajensu suka ci zarafinsu a shekarar 2020, yayin wasu mata 286 mazajensu suka ci zarafinsu a farkon zangon shekarar 2021.

Dada ya bayyana cewa shirye-shiryen karfafa gwiwa da shirye-shiryen rage talauci na ma’aikatar ya shafi rayuwar sama da mazauna 48,000 na jihar a cikin shekaru biyu da suka gabata.

A karshe tace; Hukumar WAPA zatayi aiki da sauran kungiyoyin domin rage talauci wanda hakan yana daya daga cikin abunda ke haddasa fitina a tsakanin ma’aurata.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *