fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Kirkirar ‘yansandan jihohi zai kara yawan matsalolin da ake dasu ne>>Tsohon Shugaban ‘yansanda, Idris

Tsohon Shugaban ‘yansandan Najeriya, Ibarahim Kpotun Idris ya bayyana cewa, kirkirar ‘yansandan jihohi zai kara yawan matsalolin da ake dasu ne.

 

Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Sunnews inda yace, ko kadan bai kamata a kirkiri ‘yansandan jihohi ba domin ba’a gama warware matsalar ‘yansanda a yanzu, idan aka ce za’a kirkiri ‘yansandan jihohi, matsalar karuwa zata yi.

 

Ya bayyana rashin horaswa, da karancin ‘yansandan a matsayin wasu daga cikin matsalolin dake damun hukumar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *