fbpx
Sunday, September 26
Shadow

Kisan Shugaban Fulanine ya rura wutar rikicin da ake fama dashi>>Gwamnan Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya bayyana cewa kisan wani babban shugaban Fulani a Dansadau na jiharsa ne ya kara rura wutar rikicin fulani makiyaya da manoma.

 

Gwamnan ya bayyana hakane a ta bakin kwamishinan yada labaransa, Ibrahim Dosara.

 

Da yake magana a wajan wani taro a Kaduna, ya kara da cewa, hakan yasa Hausawa da Fulani suka rika kashe juna da kaiwa juna munanan nufi.

 

Ya kuma zargi rashin yin abinda ya kamata na Sarakuna da kuma Alkalai inda yace hakan ya taimaka sosai wajan kara zuzuta wutar rikicin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *