fbpx
Friday, May 14
Shadow

Ko kun kai karata wurin Paparoma babu abunda zai min illa yabani lambar yabo>>Mbaka ya gayawa Jam’iyyar APC

Reverend Father Ekije Mbaka, Daraktan Ruhaniya na Ma’aikatar Adoration, Enugu ya kira ga jam’iyyar All Progressive Congress da suje Rome su kai kararsa wurin Paparoma.

Mbaka ya fadi haka ne a gidansa a ranar Lahadi yayi da yake gabatarwa da wata lacca ta Lahadi.

Mbaka ya kara da cewa Paparoma zai ba shi lambar yabo a lokacin da (Paparoman) ya ji cewa shi (Mbaka) yana sukar mummunar gwamnati.

Paparoma zai tafa min fada ba idan ya ji cewa ina kalubalantar mummunar gwamnatin Najeriya, don haka, APC na iya zuwa sukai karata a wajensa.

Ya kuma ce Paparoman na iya ba shi mukamin da ba zai iya rike shi ba saboda irin wannan gwagwarmayar da yake.

Idan zaku tuna a baya mun ruwaito cewa sakataren APC, Bulama, ya yi barazanar kai karar Rev Fr Ejike Mbaka ga Fafaroma Francis saboda ba ya nuna halaye irin na Yesu, duk da cewa Yesu ya kasance a karkashin gwamnatin zamanin kuma yana girmama ta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *