fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Ko an saukemu ba za’a kawo karshen Boko Haram ba>>Burutai

Shugaban Hafsan Soja, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana cewa bai kamata a nemi shugaban kasa Buhari ya dauki matakin tsige manyan hafsoshin tsaro ba, saboda a cewar Burutai, Buhari ne kadai ya san inda matsalar tsaro take da yadda zai magance ta. Buratai ya bayyana hakan ne a cikin wata doguwar tattaunawa da ya yi da jaridun TheCable, Thisday da kuma gidan talabijin na Arise a ranar Talata, 11 ga watan Fabarairu a jihar Legas. 

Idan ba ku manta ba, a kwanakin baya dai majalisar dokokin Nijeriya ta nemi shugaba Muhammadu Buhari da ya sallami dukkanin hafsoshin tsaron Nijeriya saboda a cewarsu shugabannin tsaron sun gaza samar da tsaron da aka nada su su samar musamman idan aka yi duba da yadda Bokop Haram ke ci gaba da kai hare-hare a arewa maso gabashin kasarnan.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Burutai ya ce bai so ya yi magana akan lamarin ba, saboda abin shima ya shafe shi. “Amma na san cewa komai ya faru, babban Kwamandan kasa ya san ina matsalar take, ya san me yake faruwa, kuma shi ya san matakin da ya kamata ya dauka, ya kamata a bar shi ya yanke hukunci. Bai kamata a tunzura shi akan wannann ba.” in ji Burutai.

Burutai ya ci gaba da cewa; ana cikin babbar matsala da bai kamata a dauke shi da wasa ba, inda ya ce; “Shiyasa idan aka ce wadansu manyan shugabanni a soji a cire su bisa kowanne dalili ma, abin zai zama wani iri, domin ba a kokarin magance abin. Ba ina cewa haka ne saboda ni ne shugaban sojoji ba, kuma ba na son na bari. A’a, ba wannann zancen ba. Abin ya wuce haka, abu ne da ya shafi kasa. Abu ne da ya shafi alfahari da kasa. Wadanda ya kamata su fi magana akan shugabannin tsaro ya kamata ya zama sun fito daga ciki ne, sune ya kamata a fi jin muryoyinsu a abubuwan da ba sa tafiya daidai, injishi.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *