fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

Ko yanzu aka ga mai Ak47 a harbe shi>>Shugaba Buhari

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ce har yanzu umurnin da ya baiwa jami’an tsaro na harbe duk wani mutum da aka samu yana amfani da bindiga samfurin Ak-47 ko ma mallakar wasu muggan makamai ba bisa ka’ida ba na nan daram.

 

Mai magana da yawun shugaban, Femi Adesina, a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, ya ce Buhari ya sake nanata wannan magana ta sa a yau Alhamis a Legas a lokacin da yake mika kayan aikin tsaro ga gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, da rundunar ‘yan sanda a yankin kudu maso yamma.

 

Majiyar ta ruwaito shugaban ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta yi aiki gadan-gadan a kan duk wanda aka samu da afka wa ‘yan sanda da kuma sauran jami’an tsaro.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *