fbpx
Thursday, July 29
Shadow

Kotu ta buƙaci Ganduje ya biya Jaafar Jaafar diyyar N800,000

Wata Babbar Kotu a Kano ta buƙaci gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya biya jaridar Daily Nigeria ta Jaafar Jaafar da kamfaninsa Penlight Media Ltd diyyar N800,000 kan ba ta lokacinsu da kuma ɓata suna.

Labarin da jaridar Daily Nigeria ta wallafa a shafinta ranar Talata ta ce “kotun ta yi watsi da buƙatar da lauyoyin Ganduje suka gabatar a ranar 28 ga Yunin 2021, suna neman a dakatar da shari’ar ba tare da bayyana dalilai ba.”

“Lauyan Daily Nigeria Muhammad Dan’Azumi ya ƙalubalanci buƙatar inda ya nemi kotun ta yi watsi da ita tare da bayyana ikirarin na Ganduje a matsayin marar tushe,” in ji jaridar.

Ta kuma ce mai shari’a S. B .Namalam ya umarci gwamnan ya biya Jaafar naira 400,000 haka kuma kamfaninsa N400,000 kan ɓata suna.

A 2018 ne Jaridar Daily Nigeria ta wallafa bidiyon da ke ikirarin nuna gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje yana soke daloli a aljihunsa, kan zargin karɓar rashawa, zargin da gwamnan ya ƙaryata.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *