fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Kotu ta dakatar da yunkurin tsige mataimakin gwamnan Zamfara, Gusau kan kin sauya sheka

Mai Shari’a Obiora Egwatu na babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da yunkurin tsige mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Mahadi Aliyu Mohammed Gusau.

Alkalin ya dakatar da ‘yan majalisar dokokin jihar Zamfara daga daukar wani mataki na tsige mataimakin gwamnan saboda kin sauya sheka daga jam’iyyar People Democratic Party, PDP zuwa All Progressive Congress, APC, tare da Gwamna Bello Matawalle .

Justice Egwatu ya bayar da wannan umarnin ne a ranar Litinin a hukuncin da ya yanke a karar da jam’iyyar PDP ta shigar.

Bayan ya saurari hujojin da wani Babban Lauyan Najeriya, Cif James Onoja Ogwu ya gabatar, alkalin ya ce damuwar da mai nema ya yi game da yunkurin tsigewar ya yi girma kuma ya dace don hana wadanda ake tuhumar aiwatar da abin da ake zargi.

Alkalin ya kuma dakatar da Babban Alkalin jihar Zamfara daga kafa duk wani kwamitin da zai binciki Gusau har sai lokacin da za a yanke hukunci kan wata sanarwa da PDP ta gabatar.

Sauran wadanda ake karar sun hada da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC), APC, Shugaban Majalisar Dattawa, Kakakin Majalisar Wakilai, Kakakin Majalisar Dokokin Zamfara da Gwamna Bello Matawalle.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *