Wata Babbar Kotun dake da mazauni a Calabar, babban birnin jihar Kuros Riba ta yanke wani mutum mai suna Isaac Evaghoghome hukuncin daurin shekara 7 da watanni 6 bisa laifin yi wa yarinya ’yar shekara 6 fyade.
Mai shari’a E. E Itace ta yanke wa Evaghoghome hukuncin shekara 7 da watanni 6 ba tare da zabin biyan tara ba a ranar Alhamis, 11 ga Fabrairu, 2021.
Isaac Evaghoghome ya amsa laifin da ake tuhumarsa na yi wa karamar yarinya yar shekaru 6 fyade.
Da yake maida martani game da hukuncin, Barrister James Ibor, shugaban kungiyar Basic Rights Counsel Initiative (BRCI) yace; hakika wannan hukuncin yayi daidai domin ya zama darasi ga wadanda ke aikata irin wadannan laifukan.