fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin daurin shekara 12 kan Jolly Nyame

Kotun Kolin Najeriya ta amince da hukuncin da kotun daukaka karar kasar ta yanke wa tsohon gwamnan jihar Taraba Jolly Nyame na zaman shekara 12 a gidan yari.

A watan Nuwambar 2018 ne ita ma kotun daukaka karar ta tabbatar da hukuncin da wata babbar kotun da ke Abuja ta yi wa tsohom gwamnan bisa samunsa da hannu a satar kudin jihar lokacin da yake kujerar gwamna.
A hukuncin da suka yanke ranar Juma’a, alkalan kotun kolin biyar sun amince da wani bangare na bukatar Mr Nyame.
Kotun kolin ta amince da bukatarsa game da samunsa da laifi da kuma yanke masa hukunci ko da yake ta ki amincewa da bangaren hukuncin wanda ya bukaci tsohon gwamnan ya biya miliyoyin naira.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *