fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Ku amince da afuwar da Pantami ya nema>>Gwamnatin Tarayya ta roki ‘yan Najeriya

Gwamnatin tarayya ta roki ‘yan Najeriya su amince da afuwar da ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Sheikh Isa Ali Pantami ya nema kan goyon bayan kungiyoyin Taliban da Alqaeda da yayi a baya.

 

Kakakin Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka inda yace shekaru 20 da suka wucene Pantami yayi waccan magana kuma gashi yanzu shekara me zuwa zai cika shekaru 50.

 

Yace tananin mutum na canjawa kuma Pantami ba zai sake fadar waccan magana ba. Yace kuma neman saukeshi da ake ba akan waccan magana bace, akan aikin da yake yi ne yanzu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *