fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

ku baiwa ko wane dan Nageriya damar daukar makami – Miyetti Allah ta fadawa Gwamnatin Tarayya

Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeder’s Association of Nigeria (MACBAN) ta shawarci Gwamnatin Tarayya da ta kyale kowane dan Najeriya ya dauke bindinga don kare kansa duba da kalubalen tsaro a kasar.

Kungiyar ta yi wannan kiran ne yayin da take mayar da martani a kan kalaman da Gwamnan Bauchi, Sen. Bala Mohammed, ya yi na cewa makiyaya suna dauke da bindigogi ne kawai don kare kansu.

Gwamna Mohammed ya sha suka sosai bayan kare hakkin makiyaya na yin amfani da AK-47 don kare kansu daga barayin shanu.

Shugaban kungiyar ta MACBAN na jihar Bauchi, Alhaji Sadiq Ibrahim Ahmed, ya fadawa manema labarai a ranar Lahadi cewa babu wani abin damuwa game da kalaman Gwamnan tunda bai ce makiyaya su je su haddasa rikici da shi ba.

A cewarsa, tunda Gwamnatin Tarayya ba za ta iya kare ‘yan kasa ba, yana da kyau kowane dan kasa ya kare kansa daga yan bindinga.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *