fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Ku kara Hakuri, nan gaba kadan za’a ga Amfanin ayyukan da Buhari ke yi>>APC ga ‘yan Najeriya

Jam’iyyar APC ta mayarwa da PDP martani kan maganar da ta yi na cewa, ayyukan su ne APC take kammalawa tana ikirarin cewa nata ne.

 

APC tace shugaba Buhari yana aiki dan kishin kasa ne shiyasa yake kammala ayyukan da PDP ta fara ta watsar duk da cewa ta shafe shekaru 16 akan Mulki.

 

Kakakin Kwamitin riko na jam’iyyar APC, John James ne ya bayyana haka ga manema labarai. Yace maganar bashi kuma da PDP ke kwakwazo akai, Gwamnatin shugaba Buhari na aiki da kudin da ta ciwo bashi akan abinda ya kamata.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *