fbpx
Wednesday, January 26
Shadow

Ku karbi katin zabe kuma ku zabi shugaba na gari>>Tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi

Kar ku zaɓi baragurbin shugabanni a 2023, Sanusi ya shawarci ƴan Nijeriya

Khalifa Muhammadu Sanusi, Babban Shugaban Jam’iyyatu Ansariddeen Attijaniyya na Ƙasa, ya shawarci ƴan ƙasa da su ka kai munzalin yin zaɓe, da su tabbatar sun zaɓi nagartattun shugabanni ba baragurbi ba a zaɓukan 2023.

Khalifan ya kuma yi kira ga ƴan Nijeriya, musamman matasa da su ka kai munzalin yin zaɓe da su je su yanki katin zaɓe, su tanade shi domin zaɓen nagartattun shugabanni a kowanne matakin mulki a kasar nan.

Khalifa Sanusi ya yi wannan kira ne a jiya Asabar a Lokoja a ranar ƙarshe ta taron kwanaki 3 na Mailidin Annabi Muhammad (SAW) na duniya karo na 4.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa taken taron na bana shine ” Duba kan Yadda Annabi ya Kyautata rayuwar Ɗan’adam.”

Sanusi, wanda shine Sarkin Kano mai murabus, ya shawarci matasa da su zaɓi nagartattun shugabanni a kowanne matakin mulki ba tare da duba da bambancin jam’iya ko addini ba.

“Idan matasan mu su ka samu aikin yi to tattalin arzikin ƙasar nan zai bunƙasa.

“Abu mafi muhimmanci shine, mu ba jam’iya ba ne, amma kuma ba za mu naɗe hannayenmu mu zama ƴan kallo a siyasa ba.

“Duk wani ɗan Tijjaniyya, da ga shekara 18 zuwa sama, ya yi maza ya je ya yanki katin zaɓe.

“Allah Ya umarce ku da ku bada amanar ku ga waɗanda ku ka yadda da amanar su. Yanzu mun zo lokacin da al’umma su suke ɗora masu mulki a kan kujerar mulki saboda haka hakkin ku ne.

“Ban ce dole sai ɗan Tijjaniyya ko musulmi ko ɗan wata jam’iya za ku zaɓa ba, ku zaɓi mutum nagari a kowanne mataki indai nagartacce ne,” in ji Khalifa Sanusi.

Shugaban ya yabawa Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello a bisa karɓar babban taron a jihar sa da kuma bada filin da za a gina Cibiyar Addinin Musulunci ta Duniya domin karrama Sheikh Ibrahim Niass.

Ya jaddada cewa a taron an yiwa ƙasa addu’ar samun zaman lafiya, haɗin kai, haɓɓakar arziki da samun nagartacciyar ƙasa wacce shugabannin ta za su riƙa yin daidai.

A nashi jawabin, Gwamna Bello ya suffanta taron da cewa mai ɗumbin tarihi ne gare shi da al’ummar Jihar Kogi da birnin Lokoja.

Ya kuma baiyana farin cikin sa da karɓar babban taron Mauludin Annabi Muhammad (SAW) da kuma karrama Sheikh Ibrahim Niass.

Bello ya jaddada cewa, a matsayin sa na yin adalci da gaskiya ga kowa da kowa ba tare da bambancin addini ko siyasa ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *