fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Ku kiyaye saboda bala’in da aka gani na coronavirus a shekarar data gabata ba’a ga komai ba>>Gwamnatin tarayya ta gargadi ‘yan Najeriya

Gwamnatin tarayya ta gargadi ‘yan Najeriya da cewa su kiyaye game da dawowar cutar coronavirus a karo na 3.

 

Tace abubuwan da aka gani a shekarar data gabata, ba’a ga komai ba, dan haka a kiyaye kada abubuwa su kazance.

 

Hukumar yaki da cutuka ta NCDC ce ta bayyana haka a sanarwar data fitar inda tace da yawan ‘yan Najeriya na nuna halin ko in kula game da cutar ta coronavirus da kiyaye dokokinta.

 

Shugaban Kwamitin yaki da cutar kuma sakataren Gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya bayyana cewa, dawowar cutar yasa ana samun mutane 500 a kullun suna kamuwa da ita.

 

A jihar Legas kuwa, mutane 30 ne suka mutu tun bayan dawowar cutar da aka ce ta fi ta baya saurin yaduwa da illa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *