Shugaban ‘yansandan Najeriya, IGP Muhammad Adamu ya gayawa ‘yansanda cewa su rika harbin ‘yan IPOB idan suka kawo musu hari.
Ya bayyana hakane a yau Talata bayan ziyyarar da ya kai hedikwatar ‘yansanda dake Owerri inda ‘yan Bindiga da ake zargin ”yan IPOB ne suka kai masa hari.
Yace bai inda ‘yan IPOB din zasu boye musu, sai sun zakulo su an hukuntasu.