fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Ku roki Shugaba Buhari da ya gaggauta yin murabus – HURIWA ta fadawa yan Najeriya

Kungiyar Marubutan Kare Hakkin Dan Adam ta Najeriya, HURIWA, ta fadawa ‘yan Najeriya su roki Shugaba Muhammadu Buhari da ya gaggauta yin murabus.

Kungiyar tace ta damu irin yadda harkar tsaro ke kara tabarbarewa a Arewa maso Yamma musamman a Jihohin Katsina, Neja, Zamfara da kuma hare -haren bama -bamai da Fulani ke kaiwa a wasu sassan Kudancin Kaduna.

HURIWA ta yi gargadin cewa Najeriya ta komawa kamar dusar kankara dake cikin wani babban sararin da ba a san shi ba wanda ke buƙatar haɗin gwiwar shugabannin Duniya da Majalisar Dinkin Duniya don hana rushewar dimokiradiyya ta tsarin mulki.

HURIWA ta ce tunda Buhari baya bin shawara wajen nadin Shugabannin tsaro kuma tunda nadin nasa da yayi na son rai a cikin shekaru 6 yayi nuna gazawarsa, abunda ya dace shi ne yan Nageriya su roki shi da ya gaggauta yin murabus cikin mutunci.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *