fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

Ku rufe shafin Buhari a dandalinku – Fayose ya fada wa Instagram, Facebook da sauran dandalin sada zumunta

Biyo bayan shawarar da Gwamnatin Tarayya ta yanke na dakatar da ayyukan Twitter a Najeriya bayan da dandalin ya goge sakonnin Shugaba Buhari da ke nuni da yakin Basasa, tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya yi kira ga Twitter da sauran shafukan sada zumunta da su goge asusun Shugaba Buhari.

Yace bai kamata Gwamnatin Tarayya ta rufe shafin sada zumunta na Twitter ba domin tana da daya daga cikin hanyar da suke bayyana ra’ayinsu da kuma neman yancin su.

Don haka, Twitter, Facebook, Instagram da sauran kafafen sada zumunta ya kamata su daina amfani da duk asusun da ke da alaka da @ MBBuhari da gwamnatinsa kamar yadda aka yi a Turkiyya a shekarar 2020 domin a samu zaman lafiya a Najeriya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *