fbpx
Thursday, July 29
Shadow

Ku sa ido don duba sabon wata – Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar koli kan Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), Sa’ad Abubakar III, ya bukaci al’ummar Musulmi su fara sa ido kan ganin sabon jinjirin watan Dhul Hijja 1442AH wanda zai fara daga Asabar (a yau) ).

Sarkin ya bayar da wannan umarnin ne a ranar Juma’a a cikin wata sanarwa da Shugaban Kwamitin Shawara kan Harkokin Addini, Majalisar Masarautar Sokoto, Farfesa Sambo Junaidu ya bayar ga manema labarai.

A cewar sanarwar, shugaban na musulmin ya yi addu’ar Allah ya taimaki musulmai wajen sauke nauyin da ke kan su na addini kamar yadda ake fata daga gare su.

Sanarwar ta karanta a wani bangare, “Wannan shi ne sanar da al’ummar Musulmi cewa ranar Asabar 10 ga Yuli, wacce tayi daidai da ranar 29 ga Dhul Qadah 1442AH zata kasance ranar neman sabon watan Dhul Hijja 1442AH.

“Don haka, ana neman Musulmai da su fara neman sabon wata a ranar Asabar sannan su kai rahoton ganin sa ga Hakimin na kusa don sadarwa ga Sarkin Musulmi”.

Watan Dhul Hijja na wakiltar wata na 12 a kalandar Musulunci, wata mai alfarma lokacin da Musulmi ke yin Hajji.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *