fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Kotu ta dakatar da Majalisar Tarayya da biyan kanta Albashi

Babbar Kotu a Abuja ta bayyana cewa, majakisar tarayya bata da Hurumin iya kayyade albashin ‘yan majalisar.

 

Tace hukumar kula da kudin shiga da sauran al’amuran da suka shafi kudi ne ke da wannan hurumi.

 

Alkalin kotun, Chuka Obiozor ne ya bayyana wannan hukunci, lauyiyi 2 ne suka shigar da karar dan neman a hana majalisa ta rika biyan kanta Albashi.

 

SERAP, Femi Falana da sauransu na daga cikin wanda suka rika caccakar maganar biyan Albashin ds majalisa kewa kanta.

 

A shekarar 2018, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa, kowane dan Majalisa ana bashi kudin aiki Miyan 13.5 da kuma Albashinsa na 750,000 duk wata.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *