fbpx
Saturday, June 19
Shadow

Ku Tabbatar Kun Fitar Da Zakkatul-Fitir, Sakon Sheik Bala Lau Ga Masu Hali

Shugaban JIBWIS Imam Abdullahi Bala Lau ya bukaci duk mai sukuni ya tabbatar da fitar da Zakatul fitr don tallafawa dimbin masu bukata. Shehun malamin ya ce wannan zakkah ta na da tasirin gaske ga gidaje da dama da kan kwana ba tare da tabbacin samun abun da sa a girka ba.

Malamin ya bukaci gaggauta fitar da zakkar don marar sa galihu da ma marayu su samu abinci kamar sauran jama’a a ranar sallah. Baya ga ma zakkar, malamin ya ba da shawarar ihsani na kudin cefane ga wanda ke da hali don ya zama gidajen makwabta duk su samu miya mai armashi. Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce mai yin sadaka don neman yardar Allah na daga cikin mutum 7 da za su shiga inuwar al’arshi ranar kiyama.

Rariya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *