fbpx
Monday, September 27
Shadow

Ku tsananta addu’a, ku roƙi Allah ya kawo ƙarshen rashin tsaro – Gwamna Matawalle ga ‘yan Najeriya

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya bukaci ‘yan Najeriya da su tsananta addu’o’in neman Allah ya shiga lamarin rashin tsaro.

Matawalle yayi Magana yayin wata addu’a ta musamman da kwamitin tuntuba na Ulamau (UCC) ta shirya.

Gwamnan ya halarci zaman na ranar Laraba da aka gudanar a babban Masallacin Gusau, NAN ta ruwaito.

Ya yi kira ga ‘yan kasa da su taimaka wa gwamnati da hukumomin tsaro a kokarin da suke yi na magance yan bindiga da sauran kalubale.

”Addu’a ita ce kawai makami mai ƙarfi wanda zai iya magance kowane bala’i a kan mutane. Dole ne mu nemi gafarar Allah, ”in ji Matawalle.

An gudanar da addu’o’i a dukkan masallatan Juma’a na Zamfara.

Kwamishinan ‘yan sanda, Ayuba Elkanah ya shawarci jama’a, iyaye da dangin daliban da ka sace kwananan “ da su yi hakuri su ci gaba da addu’a don samun nasarar aikin ceton ”.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *