fbpx
Monday, September 27
Shadow

Ku yi ta ce mana ‘yan amshin shata amma ba zamu yi fada da Buhari ba>>Sanata Kalu

Sanata Orji Kalu na majalisar dattijai ya bayyana cewa ba zasu taba amincewa da fada da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba.

 

Yace mutane na ce musu ‘yan Amshin shatan shugaban kasa ne amma ba gaskiya bace.

 

Yace abinda suke son fada shine ba fada ne aikinsu da shugaban kasa ba, aikinsu shine su taimakawa shugaban kasa a yiwa ‘yan Najeriya aiki. Idan yaki suke son yi, sai su shiga aikin soja.

 

Ya kara da cewa, kuma akwai abubuwan da shugaban kasar ya aika musu amma suka ki amince masa, ba tare da an ji kansu ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *