Tsohon mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana cewa, ‘yan Najeriya musamman Kiristoci su tashi su yiwa kasa addu’ar zaman Lafiya.
Ya bayyana hakane a sakon Easter da ya aike inda yace lokaci ne da ya kamata a yi amfani dashi waja yiwa kasa addu’a ba shagali kadai ba.
Yace Allah ya umarcemu da mu so makwabtanmu kamar yanda muke son kan mu. Da hakane yace yana kira ga ayi soyayyar juna.
“Therefore, on this occasion of Easter celebration, I urge all Nigerians to take time to pray first of all for peace to return to the country and also for unity.
“Nigeria is at the precipice of insecurity, poverty and, most unfortunately, disunity. These are challenges, not impediments.