fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Kudin gyaran harkar ilimi sun yi yawa, ba zamu iya ba>>Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ba zata iya samar da kudin gyaran ilimi ba a kasarnan.

 

Yace yawan kudin gyaran ilimin ya karu saboda jami’o’in sun karu. Shugaban ya bayyana hakane a jami’ar UNN Nsukka wajan yaye daliban jami’ar.

 

Yace kudin da gwamnati ke samu sun ragu matuka dalilin zuwan cutar coronavirus.  Karamin Ministan Ilimi, Emeka Nwajuiba ne ya wakilci shugaban a wajan taron.

 

Ya bayyana cewa, amma Gwamnati zata yi iya kokarinta wajan ganin ta samar da kudin kyautata ilimin manyan makarantu.

I am optimistic that the on-going drive to diversify the national economy will provide the government with additional resources to improve funding for the education system,” he said.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *