fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Kudu da Arewa sun hada kai suna goyon bayan Abba Kyari kan zargin da ake masa

Zargin Babban dansanda, DCP Abba Kyari da alaka da gawurtaccen dan damfarar nan,  Hushpuppi ya jawo cece-kuce sosai a Najeriya.

 

Saidai mafi yawa suna goyon bayan Abba Kyari kan wannan lamari inda suke bayyana cewa, basu yadda yana da alaka da Hushpuppi ba.

 

Amma kuma ba ‘yan Arewa bane kadai suke nuna goyon baya ga Abba Kyari ba hadda ‘yan kudu, duk da yake cewa akwai wanda basa tare dashi.

 

Misali, Tsohon Ministan sufurin jiragen sama,  Femi Fani Kayode ya bayyana cewa idan ba shaida ya gani karara ba, ba zai yadda Abba Kyari na da alaka da Hushpuppi ba.

 

Wani dake tare da shahararren mawaki Davido, me suna Israel ya bayyana cewa shima yana tare da Abba kyari.

 

Hakanan a shafukan sada zumunta da yawa ma an samu masu goyon bayan Abba Kyari inda suke cewa basu yadda yana da alaka da damfara ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *