fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Kuma Dai: An fito da wani sabon Kazafi akan Sheikh Pantami

Baya ga zargin cewa yana goyon bayan kungiyoyin ta’addanci a shekarun baya wanda kuma ya warware lamarin a wani jawabi da yayi, an sake fito da wata sabuwar magana mara dadi da ake zargin Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Sheikh Isa Ali Pantami.

 

Jaridar People’s gazette ta ruwaito cewa wai Sheikh Pantami a shekarun baya, ya Shirya kashe tsohon gwamnan jihar Kaduna, Patrick Ibrahim Yakowa.

 

Jaridar ta bayyana cewa a shekarar 2010 ne Sheikh Pantami ya jagoranci zaman taron da sauran wasu membobin kungiyar JNI. Ta wallafa wata takarda wadda ta yi ikirarin cewa itace aka cimma matsaya a wajan taron. Ta kuma bayyana cewa ta nemi jin ta bakin Minista akan wannan zargi amma bai ce komai ba.

 

A kwanakinnan dai an sako Ministan gaba ana ta dangantashi da abubuwan bata suna, musamman daga jihohin Kudu, inda wasu ke ta kiran cewa ya sauka, ciki hadda gwamnan Rivers, Nyesome Wike.

 

Ga wanda ke son karanta cikakken labarin yana iya bin wannan link din na kasa.

 

https://www.gazettengr.com/document-shows-how-pantami-plotted-assassination-of-former-kaduna-governor-patrick-yakowa/?

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *