fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Kuma Dai: Iran ta sake kaiwa Kasar Amurka hari

Awanni kadan bayan da shugaban kasar Amurka, Donald Trump yayi jawabin cewa ga dukkan alama kasar Iran ta saduda da shiga yakin soji da kasar ta Amurka, Iran din ta kaiwa Amurkar hari a karo na biyu.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Harin wanda shine na biyu bayan wanda Iran din ta kai kan sansanin sojojin kasar ta Amurka a Iraqi ranar Talata, ya zone a jiya, Laraba inda Iran ta harba rokoki 2 cikin ofishin jakadancin kasar Amurkar dake Iraqi.

Saidai Rahoton sojojin Iraqi yace babu wanda ya rasa ransa a harin.

Reuterz ta ruwaito cewa zuwa yanzu dai babu wata sanarwa daga bangaren kasar Amurka akan sabon harin da Iran din ta kai musu.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *