fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Kuma Dai:Kalli Abinda me shafin Twitter yace akan Zanga-Zangar June 12 da ake ganin na iya zama tsokanar Gwamnati

A yayin da hukumomi suka shirya Murkushe masu Zanga-Zangar June 12 ta ranar Dimokradiyya inda Gwamnoni da dama suka yi kiran kada a yi, kuma wasu kungiyoyin fafutuka suka janye.

 

Kasar Amurka ma ta bada shawarar kada a yi Zanga-Zangar amma me Shafin Twitter,  Jack Dorsey ya nuna goyon bayansa ga Zanga-Zangar.

 

Ya saka Tutar Najeriya a shafinsa wanda hakan wasu suka fassara shi da cewa yana goyon bayan Zanga-Zangar ne.

Hakan dai ka iya kara tsamin Dangantaka tsakaninsa da Gwamnatin Tarayya wadda yanzu haka ta dakatar da amfani da Twitter a Najeriya, sama da mako daya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *