fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Kumadai: Wata bakuwar cuta ta bulla a Benue

Hukumomin lafiya a Najeriya sun tabbatar da cewa kwararru na gudanar da bincike kan wata bakuwar cuta, wadda ake zargin ta halaka akalla mutum goma sha biyar a jihar Binuwai.

Sakamakon wasu bayanai daga dakin bincike na kimiyya ya nuna cewa, bakuwar cutar ba ta zazzabin Lassa ba ce.
Haka kuma, ana zargin fiye da mutum dari ne suka kamu da cutar da alamunta ke nuna kumburin kafa da ciki.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ministan lafiya na Najeriya, Dakta Osagie Ehanire ya shaida wa BBC cewa ana zargin mutane sun ci wani kifi ne da suka kama a wani rafi da aka zuba wa guba.

“Ana amfani da wata guba ta hanyar watsa ta a cikin rafi kuma sai su kama kifin su ci,” in ji shi.

Ya ce hakan na da matukar hadari ga lafiyar dan Adam.

Dakta Osagie ya ce hukumomin lafiya da ke tashohin jiragen Najeriya a shirye suke tsaf don tunkarar duk wata cuta da ake iya shigowa da ita kasar.

Ya ce suna bincike “don gano mara lafiya a cikin fasinjoji masu shigowa daga wata kasa.”

Ministan ya ce duk da rahotannin da wasu kafofin yada labarai ke watsawa na cewa cutar ta samu wuri a jihar Binuwai, har yanzu ba a kai ga tantance yawan asarar rayukan da cutar ta sa aka yi ba.

Sannan ya ce mutane su kwantar da hankalinsu don har yanzu babu billar cutar coronavirus a kasar.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *