fbpx
Thursday, May 6
Shadow

Kungiyar ACF Ta Bukaci Buhari Ya Kara Tsawaita Dokar Hana Jiragen Sama Shawagi Zuwa Ga Jihohin Binuwai, Taraba, Da Borno

Kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) ta roki Shugaba Muhammadu Buhari da ya tsawaita dokar hana zirga-zirgar jiragen sama da aka kakaba wa jihar Zamfara a kwanan nan zuwa wasu jihohin da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga.
A ranar Talata ne Shugaba Buhari ya ayyana Zamfara a matsayin “yankin da jiragen sama ba za su ratsa shi ba” ya kuma haramta duk wasu ayyukan hakar ma’adanai a jihar.
Umarnin, wanda mai bai wa Shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Babagana Monguno ya bayyana, ya biyo bayan sakin daliban 279 na Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Jangebe a karamar Hukumar Talata-Mafara da ’yan bindiga suka sace tun farko.
A wata sanarwa a ranar Laraba, Shugaban ACF, Audu Ogbeh, ya yaba da umarnin kuma ya yaba da sakin ‘yan matan.
Cif Ogbeh, duk da haka, ya ce akwai bukatar yin irin wannan umarnin a wasu jihohi kamar Benuwai, Taraba da Borno inda ake ta rade-radin cewa jirage masu saukar ungulu suna yawan ajiye makamai don ‘yan fashi da masu tayar da kayar baya.
An fitar da sanarwar ta bakin kakakin ACF, Emmanuel Yawe, a Kaduna.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *