fbpx
Wednesday, December 1
Shadow

Kungiyar Boko Haram na karbar Zakka da haraji a hannun mutane

Kungiyar Boko Haram na tursasawa mutane biyan Haraji da Zakka a wasu yankunan da take da iko a jihar Borno.

 

Mutane daga Damboa, Musamman manoma sun tabbatarwa da Daily Trust faruwar hakan.

 

Wani jami’in gwamnati ya bayyana cewa, Boko Haram na barin mutane su yi noma amma kuma daga karshe suna karbar kudin haraji daga hannayen mutanen.

 

Majiyar tace a baya, zamanin mulkin Shekau, baya barin mutane su je gona amma a ISWAP ta kwace iko da yankin, tana bari a je gona amma tace dolene a biya zakka.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *