fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Kungiyar Boko Haram ta saki sabuwar amaryar da suka sace a Borno

An saki sabuwar amaryar, Hauwa Hassan, wacce ‘yan Boko Haram suka sace a babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

An bayyana cewa yan ta’addan sun yi kwanton baunar ga motocin da ke bin babbar hanyar a ranar Juma’a, 26 ga watan Fabrairu, kuma suka sace amaryar, kawayenta da matafiya da yawa.

Amaryar da kawayenta na kan hanyarsu ta zuwa Damaturu bayan bikinta a Maiduguri, babban birnin jihar Borno lokacin da lamarin ya faru.

An tattaro cewa maharan sun sauke mutanen ne a wani kauye kusa da Damaturu, babban birnin jihar Yobe, da tsakar dare, babu tabbacin ko an biya kudin fansa.

Babagana Kashim, daya daga cikin dangin wanda lamarin ya rutsa da shi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, ya ce a halin yanzu amaryar da kawayenta suna kwance a wani asibiti dake Damaturu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *