fbpx
Monday, November 29
Shadow

Kungiyar Dattijan Arewa bata da goyon bayan Ainahin dattijan Arewa kuma dama can bata goyi bayan shugaba Buhari ba>>Fadar shugaban Kasa

Fadar shugaban kasa ta mayarwa da kungiyar dattijan Arewa da martani kan cewa da ta yi shugaba Buhari ya gaza akan harkar tsaro. 


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

A sanarwar data fito ta bakin me magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina, fadar shugaban kasar ta ce kungiyar Dattawan Arewa ta Northern Elders Forum ta mutum daya ce kuma ra’ayinshi take bi,bata da wasu Membobi da za’a ce tana wakiltar Ainahin dattawan Arewa.

Adesina ya kara da cewa, Kungiyar ta Ango Abdullahi a zaben 2019 ta nuna karara bata tare da shugaba Buhari inda ta goyawa wani dan takara daban baya kuma dan takarar bai yi nasara ba.

Adesina ya bayyana cewa kungiyar ta NEF kamar Janar din sojane da bashi da Dakaru.

Ya kara da cewa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari abinda yasa gaba shine gyaran kasa kuma ‘yan kasa na gari sun san ainahin yanda halin da kasar ke ciki dan haka basa bukatar kungiyar ta dattijan Arewa ta gaya musu komai.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *