fbpx
Wednesday, December 1
Shadow

Kungiyar Dattijan Arewa da Jama’atu Nasril Islam sun goyi bayan shugaba Buhari kan cewa Boko Haram ba Kiristoci tafi kaiwa hari ba

Kungiyar jama’atu Nasirl Islam karkashin jagorancin me Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar na III ta bakin sakatarenshi,Abubakar Khalid Aliyu ya bayyana cewa maganar da shugaba Buhari yayi kan cewa kaso 90 na Harin Boko Haram akan Musulmai yake karewa gaskiyane.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Yace musulmai dake Karatun Boko ne kumgiyar Boko Haram ta fi kaiwa hari inda yace da Kiristoci suke nufa da harinsu da sun rika kai musu Hari ta ko’ina.

Akan maganar da kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN ta yi kuwa na cewa kalaman shugaban kasar abin ban haushine, Abubakar ya bayyana cewa ya kamata ifan shuwagabanni zasu yi magana su rika taunawa, yace yanzu misali ka je gurin ‘yan gudun Hijira kaga wanda suka fi shan wahala.

Itama Kungiyar Dattijan Arewa ta hannun Sakatarenta, Anthony Sani ta bayya a cewa, tana goyon bayan shugaban kasar akan kalaman nashi na cewa Kungiyar Boko Haram ba kitistoci ta fi kaiwa hari ba.

Yace Mafi yawan ‘yan kungiyar musulmi ne da suka fito daga yankin Arewa maso gabas, hakanan ma wanda suka kaiwa hari. Ya kara da cewa itafa Boko Haram ba wani Jihadin da take kungiyace dake son cimma wasu muradu na son Ranta.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *