fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Kungiyar Kiristoci ta CAN ta dakatar da faston da ya jinjinawa Sheikh Pantami

Kungiyar Kiristocin Najeriya,  CAN ta dakatar da fastonta na jijar Gombe saboda jinjinawa Sheikh Pantami.

 

Kungiyar tace Rev. Sunday Congo ya jinjinawa Sheikh Pantami ba tare da saninta ba.

 

Kungiyar tace amfani da sunanta da faston yayi wajan taya Pantami Murna bai mata dadi ba sannan kuma hakan ya jawo cece-kuce sosai a tsakanin membobinta.

 

Sannan kuma ba da amincewarta yayi hakan ba.

 

Shidai, Rev. Sunday Congo ya taya Sheikh Pantami murnane bayan da aka bashu mukamin Farfesa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *