fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Kungiyar Kiristoci ta CAN ta karyata maganar shugaba Buhari na cewa kaso 90 na harin Boko Haram Musulmai yake shafa

Kungiyar Kiristocin Najeriya ta CAN ta karyata maganar shugaban kasa, Muhammadu Buhati da yayi ta cewa kaso 90 cikin dari musulmaine harin Boko Haram ke shafa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

CAN ta bayyana hakane ta bakin sakataren hulda da jama’arta, Kwamkur Samuel inda ya bayyana cewa kalaman na shugaba Buhari abin ban haushine, karyane kuma na kawar da hankalin jama’a.

Yace shin wai ma ana gasar yawan wanda ke garin ke shafane tsakanin musilmai da kirista. Sannan idan shugaban da gaske yake to ya basu hujja a zahirance na ikirarin nashi. Samuel ya kara da cewa shugaba Buhari na amfanine da rahoton da jami’an tsaro ke kaimasa shi yasa yake wannan magana amma idan ma da za’a hada duka musulman da aka kashe da ma ‘yan Boko Haram din da sojojin suka kashe basu kai rabin yawan kiristocin da rikicin na Boko Haram ya shafa ba.

Ya kara da cewa kalaman na shugaba Buhari sun fito fili da irin fifikon da ake baiwa mayakan Boko Haram kan wadanda ke sansanin gudun hira da hare-haren kungiyar ya shafa da sunan canja dabi’a.

Yace shin wai akwai wata rayuwa data fi soyuwa ga shugaban kasarne?

Samuel yace idan ‘yan Najeriya basu sani ba to bari ya gaya musu dalilin da yasa har yanzu shugaba Buhari bai cika alkawarin daya dauka na kubuto ‘yan matan Chibok daga hannun Boko Haram ba wanda tun kamin ya hau mulki aka sace su amma kuma aka yi gaggawar kwato ‘yan Matan Dapchi banda Leah Sharibu wadda Kiristace, dalilin inji Samuel shine saboda yawancin ‘yan matan Chibok Kiristochine yayin da su kuma matan Dapchi musulmai ne.

Ya kara da cewa abin kunyane ace irin wadannan kalaman na fitowa daga mutun me daraja ta daya a kasarnan, Samuel yace kamata yayi gwamnati ta baiwa kiristocin kasarnan hakuri bisa gazawar da ta yi na kare rayukansu.

Samuel yace tabbas akwai tsirarun musulmai da Boko Haram din ta kaiwa Hari a masallatai wanda kuma sukar Akidar kungiyar da suka yi ne ya jawo haka.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *