fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Kungiyar Kwadago tace bata yadda da cire tallafin Man fetur ba,Masana sun ce dubu biyar da Gwamnati zata rabawa ‘yan Najeriya shiriritace

Masana a bangaren tattalin arziki sun soki shirin gwamnatin tarayya na rabawa talakawa Dubu biyar duk wata idan ta cire tallafin man fetur.

 

Gwamnatin tace zata yi hakane dan saukakawa ‘yan Najeriya wahalar da zasu sha idan ta cire tallafin man.

 

Saidai masanan sun ce maganar rabawa ‘yan Najeriya Dubu 5 duk wata ba zata taba ije musu wahalar da zasu sha idan an cire tallafin man fetur ba.

 

Shima shugaban kungiyar Kwadagi ta kasa, Ayuba Wabba yace basa maraba da cire tallafin Man fetur din saboda zai jawo tsadar rayuwa.

 

Hakanan yace cire tallafin ba karamar kara matsalar tsaron da ake fama da ita zai yi ba kuma zai iya sawa awa gwamnati bore.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *