fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Kungiyar likitocin Najeriya, NMA ta baiwa gwamnatin Zamfara wa’adin makonni biyu don magance matsalar rashin tsaro

Kungiyar Likitocin Najeriya (NMA) reshen jihar Zamfara ta koka kan halin rashin tsaro da ake samu a jihar, inda ta bai wa gwamnatin jihar wa’adin makonni biyu don magance bala’in.

Shugaban kungiyar, Dr Manor Nature Tsafe ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Gusau, babban birnin jihar, a hedikwatar NMA.

A cewarsa, ayyukan ‘yan bindiga sun zama matsala ga masu aikin likitanci a jihar, yana mai jaddada cewa babu wani likita da zai yi farin cikin yin aiki a cikin yanayi mara tsaro.

“Don haka kungiyar tana ba gwamnatin jihar wa’adin makonni biyu don magance matsalar rashin tsaro a jihar,” in ji shi.

Dakta Tsafe ya yi bayanin cewa yanzu haka likitoci da ma’aikatan aikin jinya sun zama abin kama ga ‘yan fashi a jihar.

Shugaban ya yi gargadi kan shirin da ‘yan bindiga ke yi na sace karin likitoci da ma’aikatan jinya a asibitoci daban -daban na jihar.

Ya yi barazanar cewa kungiyar ba za ta yi aiki cikin dare ba, yana mai nuni da cewa idan gwamnati ba ta magance matsalar ayyukan ‘yan fashi ba, za a rufe kowane asibiti da karfe 6 na yamma a kullum.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *