fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Kungiyar ma’aikatan shari’a ta Najeriya za ta fara aikin sai baba ta gani

Kungiyar ma’aikatan shri’a ta Najeriya ta shirya tsunduma cikin yajin aikin sai baba ta gani daga ranar 6 ga watan Afrilun da muke ciki.

Wanann umarni na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren kungiyar ta JUSUN Isaiah Adetola ya fitar.

Sanarwar ta ce maganar yajin aikin ta samo asali ne tun a bayanin bayan taron da aka yi da kwamitin zartarwa na kasa da kungiyar a ranar 31 ga watan Maris a Abuja.

Sanarwar ta ce da an tsara fara yajin aikin ne a ranar 5 ga watan Afrilu amma dole aka matsara da shi zuwa ranar Talata 6 ga watan Afrilun 2021 saboda hutun da aka bayar a kasar.

Kungiyar dai sai da ta bai wa gwanati wa’adin kwana 21 domin ta biya musu bukatarsu na bai wa bangaren shari’a cin gashin kai a harkokin kudi kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya zayyana.

Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta kasar ta fara na ta yajin aikin saboda da nata bukatun da ke da alaka da kudade.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *