fbpx
Friday, May 14
Shadow

Kungiyar NVMA reshen Jihar Sakkwato tayi bikin ranar likitocin dabbobi ta duniya

Kungiyar likitocin dabbobi ta Najeriya reshen jihar Sakkwato (NVMA) ta yi bikin ranar dabbobi ta duniya ta 2021, wanda galibi ke zuwa duk Asabar din karshen kowane watan Afrilu.

Ranar likitocin dabbobi ta duniya rana ce da kungiyar likitocin dabbobi ta duniya ta ware domin murnar gudummawar da likitocin suke bayarwa a fadin duniya.

Tun daga shekara ta 2000, ana yin bikin a ranar Asabar ɗin ƙarshe na kowane watan Afrilu.

Taken bikin na bana, a cewar wata sanarwa da Shugaban da Sakatare Janar na NVMA reshen Sakkwato, Dakta Mubarak M. Bello da Dakta Attahiru Ahmad R. a garin sokoto, shi ne ”Martanin likitocin dabbobi game da cutar COVID -19″.

Yace kungiyar reshen Jihar Sakkwato sun taka muhimmiyar rawa wajen dakile yaduwar cutar ta hanyar wayar wa mutane kai, tabbatar da tsabtar mahauta da sauran wurare.

Kungiyar ta kuma yaba wa gwamnatin jihar Sakkwato, da kwararrun likitocin ta, da duk wasu masu ruwa da tsaki bisa kokarin suke yi na dakile yaduwar cututtuka a cikin jihar, yayin da kuma ta bukaci al’ummar Jihar da su bada hadin kai wajen karbar allurar rigakafin Covid-19.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *