fbpx
Saturday, June 19
Shadow

Kwalejin Nuhu Bamali Polytechnic ta dakatar da ayyukan karatun

Hukumar kula da kwalejin fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zariya a jihar Kaduna a ranar Alhamis din da ta gabata ta sanar da dakatar da aiyukkan karatun ta sakamakon harin da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai wa makarantar.

Malam Mahmud Kwarbai, jami’in yada labarai da sadarwa na hukumar ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a.

An ruwaito cewa wasu da ake zargin ‘yan fashi ne sun kai hari makarantar, sun kashe dalibi guda, sun yi awon gaba da ma’aikata biyu da wasu daliban.

Kwarbai ya ce harin ya haifar da mummunan tashin hankali a tsakanin daliban, saboda haka dakatar da ayyukan ilimi a makarantar.

Jami’in yada labarai na cibiyar ya lura cewa an umarci ɗalibai su bar makarantar nan take.

Ya ce, an cire daliban IJMB saboda jarabawar da Jami’ar Ahmadu Bello za ta fara, za ta fara ne a ranar 15 ga Yuni.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *